Hukumar zabe a Najeriya na neman dage lokacin zaben badi

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Farfesa Attahiru Jega

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta, INEC, ta ce tana duba duk wasu hanyoyin shari'a, domin dage lokutan gudanar da zaben gama garin da ake shirin yi a kasar, a watan Janairu mai zuwa.

In ji INEC din, tana bukatar lokaci domin gudanar da rajistar masu zabe, su kimanin miliyan saba'in.

To amma duk da haka, har yanzu hukumar na nan kan shirin rantsar da sabon shugaban kasar a watan Mayu, ko da kwa an jinkirta zabubukan.

Tun farko dai, babban mai baiwa shugaban Najeriyar, Goodluck Jonathan shawara ta fuskar tsaro, Janar Aliyu Gusau mai ritaya, yayi murabus daga mukamin, domin shi ma ya shiga takarar shugabancin kasar.

Janar Aliyu Gusau, wanda Musulmi ne daga yankin arewacin Najeriyar, yayi sanarwar ce, kwana daya bayan da shugaba Goodluck Jonathan ya kaddamar da kamfen din takarar sa.

Bayan rasuwar shugaba Umaru Musa 'Yar Adua a watan Mayu ne Dr. Goodluck Jonathan, wanda Krista ne daga kudancin Najeriya, ya zama shugaban kasar.

Ana ganin shugaba Goodluck Jonathan zai fuskanci babban kalubale daga wasu 'yan jam'iyyarsa ta PDP, 'yan arewacin kasar, wadanda su ma suke neman yin takarar shugabancin Najeriyar, a karkashin tutar jam'iyyar.