China ta dakatar da hulda tsakanin jami'anta da na Japan

Jirgin ruwan da ya janyo takaddama tsakanin China da Japan
Image caption Jirgin ruwan da ya janyo takaddama tsakanin China da Japan

China ta dakatar da duk wata hulda tsakanin manyan jami'an gwamnatin ta da na Japan.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da wata kotu a Japan ta yanke, cewa a cigaba da tsare kyaftin din wani jirgin ruwa na kamun kifi, dan kasar Chinar, wanda aka kama a farkon wannan watan, a wani yankin ruwaye da ake takaddama a kai.

Ma'aikatar harkokin wajen Chinar ta kuma ce, ta dakatar da shawarwarin da take yi da Japan, game da kara yawan zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasashen biyu.

Japan tayi kiran da a kwantar ta hankali.

Ta ce za a yi wa kyaftin din shari'a, kamar yadda dokokin kasar suka tanada.

Jirgin ruwansa ya ci karo da jiragen ruwan Japan masu yin sintiri ne, a wani yankin da ke kusa da rijiyoyin mai da na iskar gas da ke karkashin teku, wadanda dukan kasashen biyu ke neman tonowa.