China ta dakatar da hulda tsakanin ministocinta da na Japan

Jirgin ruwan da ya janyo takaddama tsakanin China da Japan
Image caption Jirgin ruwan da ya janyo takaddama tsakanin China da Japan

Kafofin yada labaran gwamnatin China sun ce, Chinar ta dakatar da duk wata hulda tsakanin ministocin ta da na Japan.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da wata kotu a Japan ta yanke, cewa a cigaba da tsare kyaftin din wani jirgin ruwa na kamun kifi, dan kasar Chinar, wanda aka kama a farkon wannan watan, a wani yankin ruwaye da ake takaddama a kai.

Gidan talabijin din Chinar ya ce, kasar ta kuma dakatar da shawarwarin da take yi da Japan, game da kara yawan zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasashen biyu.

Tun farko, ma'aikatar harkokin wajen China ta bukaci Japan ta sako Kyaftin din jirgin ruwan.