An kama yan fashi da makami a jihar Abiya

Image caption Wasu jami'an yansanda a Najeiya

A Najeriya, rundunar 'yan sandan jihar Abiya ta ce, ta kama wasu mutane goma bisa zargin aikata fashi da makami, ciki har da wasu jami'an 'yan sanda biyu.

Wannan al'amari dai ya zo ne bayan wani tabbaci da hukumomin 'yan sandan Najeriya suka bayar cewa, suna gudanar da bincike game da zarge-zargen da ake yi wa wasu jami'ansu da hannu a batun sace mutane ana garkuwa da su don neman fansar kudi.

Mista Jonathan Johnson wanda shine kwamishinan yansanda a jihar Abiya ya ce, mutanen da aka kama sun hada da fararen hula su takwas da kuma wasu jami'an 'yansanda biyu, dayan mai mukamin saja dayan kuma kopur.

Hakan kuma wata alama ce da ke nuna irin sabon salon da aikata miyagun laifuffuka ke ci gaba dauka a kasar.