'Yan gwagwarmayar Islama sun kama gidajen rediyo a Somalia

Sheikh Sharif Ahmed, Shugaban Somalia
Image caption Sheikh Sharif Ahmed, Shugaban Somalia

'Yan gwagwarmaya a Somalia sun kama wasu gidajen rediyo biyu a birnin Mogadishu, a hare-hare na baya-bayan nan da suke kaiwa kafofin yada labarai.

'Yan bindiga na kungiyar tawayen Al Shabaab sun kwace gidan rediyon HornAfrik, yayin da kuma wasu mayakan na kungiyar Hizbul Islam, suka kama gidan rediyon GBC.

Somaliya dai na da hadari sosai ga 'yan jarida.

Masu fafutukar Musulunci, wadanda ke kokarin ganin bayan gwamnatin kasar da kasashen yamma ke marawa baya, musamman sun kafawa gidajen rediyo kahon zuka.

A watan Mayun da ya wuce, 'yan bindiga sun hallaka wani fitaccen dan jarida a Somaliyar, wanda ke aiki a wani gidan rediyon da ya soke su: