An toshe rijiyar man da ta yi bindiga a tekun mexico

Hukumomin Amirka sun ce, daga karshe dai kamfanin BP ya samu ya like rijiyar man nan da ke tekun Mexico, wadda ta yi bindiga watanni biyar da suka wuce.

Hadarin ya janyo malalar mai mafi muni a tarihin Amirka.

Jami'in da ke kula da kwashe man, Thad Allen, ya ce an sami nasarar toshe rijiyar da siminti.

Ma'aikata goma sha daya ne suka hallaka, lokacin da rijiyar man ta Deepwater Horizon ta tarwatse a watan Afrilu.

Shugaba Obama ya ce, wani mahimmin ci gaba ne aka samu wajen like rijiyar.

To amma kuma akwai sauran aiki a gaba, yayin da ake maida hankali wajen sake gina wuraren da malalar man ta shafa.