Kungiyar tarayyar Afrika na bikin ranar zaman lafiya ta duniya

Image caption Membobin kungiyar tarayyar Afrika

A karo na farko a tarihi, kungiyar gamayyar kasashen Afrika na bikin ranar zaman lafiya ta duniya da fatan samun tsaiko a wuraren da ke fama da rikici don bada damar isar da agaji ga farar hula.

Gamayyar kasashen Afrikan ta yi kira ga al'umar nahiyar da su yi shiru na minti guda, domin tunawa da mutanen da aka kashe a rikice-rikicen da ake fama da su a nahiyar.

Shugaban hukumar, Jean Ping ya ce yake-yake sun ragu cikin shekaru goman da suka gabata amma rigingimu na cigaba da kamari a Somalia da yankin Darfur na kasar Sudan.