Mutanen da aka sace a Nijar suna Mali

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta ce tana kyautata zaton 'yan kungiyar Alka'ida ne ke da alhakin sace Turawan nan 'yan kasar Faransa a garin Arlit, wadanda ma'aikata ne na kamfanin hakar ma'adinai na AREVA .

Kazalika gwamnatin ta ce tana ci gaba da daukar matakan tsaro a yankin tare da gudanar da binciken da zai taimaka a gano turawan.

A kan haka ne ma wasu kwararrun sojojin Faransar su tamanin suka isa a Yamai, don taimakawa a binciken.

Yau da safe kwamitin da gwamnatin mulkin sojan kasar ta kafa domin bin diddigin satar turawan,ya yi wani taro karkashin jagorancin Praminista Dr Mahamadu Dandah domin ci gaba da yin shawarwari a kan al'amarin.