Tattalin arzikin Najeriya

Image caption Matattan man fetur

Tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka Afirka, jama'a ke dogaro kan noma, kiwo da albarkatun kasa, wannan kuma bai sha bam-bam ba a Najeriya, domin kuwa tarihi ya tabbadar da cewa noma da kiwo na daga cikin abubuwan da jama'ar kasar suka dogara akai domin samun kudaden shiga.

Hakanan kuma Najeriya ta kasance kasa mai tattare da dimbin arzikin albarkatun kasa kama daga koko, roba ko danko,man petur, gyada, auduga da dai sauransu, wadanda kasar ke fitarwa zuwa kasashen waje domin samun kudaden shiga.

Sai dai a shekarun 1970 lokacin da bukatar man petur a kasuwannin duniya ta yi matukar karuwa, gwamnati ta maida hankalinta kacokan ga batun hakar man, inda akai watsi da sauran abubuwan da ke kawowa kasar kudaden shiga, musamman gyada da auduga.

Wannan yasa wasu masana tattalin arziki ke ganin wani babban kuskure ne, ganin yadda sannu a hankali aka yi watsi da noma, lamarin da har a wannan lokaci ke yin tasiri musamman wajen samarwa kasar abinci.