Kano Dalar Gyada

Image caption Dalar gyada a Kano

A farkon shekarun 1970 lokacin da ake noma sosai a Najeriya, jahar Kano tayi suna wajen noman gyada wadda ake fitarwa kasashen waje, domin samawa kasar kudaden shiga.

A wancan lokacin 'yan kasuwa kan tara buhunan gyadar da suka sayo daga kauyukan jahar a wani katon wajen kafin a kwashe su zuwa Lagas, inda ake fitar da su ta jiragen ruwa, da hakane kuma aka rika gina dalar gyadar a Kano.

Sai dai kuma sannu a hankali wannan dalar gyadar ta bace bayan da aka mai da hankali wajen hakar man fetur da ke matukar kasuwa a kasuwannin duniya.

To ko mai ya sa dalar gyada a jahar Kano tai batan dabo? Wani babban dalilin da gwamnati da jama'a ke ganin ya kai ga hakan shine na kwarewar da jama'a sukai wajen sarrafa gyadar, sabanin a baya inda babu injina da sauransu.

Yayin da wasu kuma ke dora alhakin bacewar dalar gyadar kan man petur, wasu kuma na cewa mutuwar jiragen kasa a Najeriya ne ya hana safarar gyadar daga arewa zuwa Legas.