Harkar kiwon lafiya a Najeriya

Kafin Zuwan Turawa - lokacin da suka shigo: Hanyar kula da lafiya ta gargajiya ita ce kadai ake amfani da ita wajen kula da lafiyar jama'a a Najeriya tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka Afirka.

Kamar yadda aka san su, wadanda ke wannan aiki a wancan lokacin wato Malamai ko Boka da Unguwar Zoma a arewa, ko Adahunse,Onisegun, Babalawo a kasar Yarabawa, ko Dibia a kasar Ibo, dukkaninsu na amfani ne da hanyar gargajiya, ganyayyaki ko itatuwa wajen warkar da marasa lafiya.

Zuwan kungiyar Mishan Najeriya ne a shekarar 1850 aka fara amfani da ilimin kimiyya a fannin kiwon lafiya, wanda ya samar da hanyar kiwon lafiya ta zamani.

Bayan da turawa suka shigo suka kafa gwamnatinsu a kasar, mazauna birane ne kadai aka fi baiwa kulawa ta fannin kiwon lafiya, yayin da mazaune yankunan karkara ke dogaro da kungiyoyin mishan.

Bayan 1960: Bayan da Najeriya ta samu 'yancin kanta a shekarar 1960, yawancin asibitocin gwamnati na maida hankali ne ga ma'aikata yayin da kungiyoyin mishan su kuma ke maida hankali kan talakawa.

Tun daga wannan lokacin a iya cewa harkar kiwon lafiya ke bukatar gyara a Najeriya ta yadda gwamnati za ta hada dukkan al'umma a cikin shirinta na kula da lafiya, domin kuwa nauyi ne da ya rataya a wuyanta.

Gwamnatin Najeriya ta kasa fannin kiwon lafiya zuwa mataki 3 domin ganin ta kai ga jama'ar karkara da ma talakawan kasar wadanda ake ganin bata ba su kulawar da ta dace.

1.Hukumar kula da lafiya matakin farko: Wannan shi ne matakin farko na kula da lafiyar jama'a wanda yawancin ayyukansa ke karkashin kananan hukumomi tare da tallafin ma'aikatun lafiya na jahohi.

2. Hukumar kula da lafiya mataki na biyu: Wannan matakin na kulawa ne da marasa lafiyar da ake turawa daga matakin farko domin samun cikakkiyar kulawar da suke bukata.

Kamar wadanda ke bukatar tiyata, cutukan kananan yara da makamantansu.

A wannan matakin gwamnati kan samar da kayayykin aiki da dakunan gwaje-gwaje.

3. Manyan cibiyoyin kiwon lafiya: Wannan matakin ya kunshi manyan asibitocin koyarwa, inda ake da kwararru a fanni daban daban kamar ciwon kashi,ido, tabin hankali, kula da lafiyar mata masu juna biyu da kuma kananan yara.

Gwamnati na samar da kwararrun likitoci da kayyakin aikin da ake bukata a wannan mataki domin baiwa jama'a kulawar da suke bukata.

Sai dai kuma duk da wannan matakan da gwamnatin ta dauka, masana a fannin kiwon lafiya na ganin fannin kiwon lafiya na cikin wani mawuyacin hali, wanda suke ganin muddin gwamnati ba ta shawo kansu ba, to kuwa da wuya a samu ci gaba wajen kula da lafiyar jama'a a kasar.

Na farko dai rashin maida hankali a karkara wanda ya samo asali tun lokacin mulkin turawa wata babbar matsala ce dake haifar da yawan mace-mace, musamman na mata masu juna biyu da yara kanana.

Wata babbar matsala da fannin kiwon lafiya ke fuskanta a Najeriya ita ce ta rashin kwararrun likitoci da ingantattun kayan aiki, da kuma rashin biyan likitocin yadda ya kamata.

Wannan yasa zurarewar kwararrun likitoci daga kasar suna zuwa kasashe kamar Amurka, Turai, Afirka ta Kudu da dai sauransu.

An kiyasce cewa a shekarar 1995 kwararrun likitoci 'yan Najeriya 21,000 ne ke aiki a Amurka kadai.

Wannan yasa tilas ne gwamnati ta maida hankali wajen samar da kwararrun likitoci da ma'aikatan jiyya ta hayar basu horan da ya dace, tare kuma da biya musu bukatunsu, muddin tana son kawo gyara a fannin kula da lafiyar al'ummarta.