Kafuwar masana'antu a Najeriya

Najeriya ta kasance kasa ta 44 dake da karfin masana'antu a duniya kuma ta 3 a nahiyar Afirka. Sai dai tun bayan da kasar ta samu bunkasa ta yawan man da take tonowa sai tai watsi da masana'antun ta koma dogaro da man fetur domin samun kudaden shiga.

Masana'antar hako ma'adanai

Najeriya kasa ce da Allah Ya yi wa arzikin ma'adanai masu dinbin yawa, wadanda suka hada da Zinare,Tama da Karafa, Kwal, Kuza, Uranium da dai sauransu.

Tun a shekarar 1903 ne gwamnatin mulkin mallaka ta Birtaniya ta fara bincike kan hakar ma'adanai a yankin arewacin Najeriya, kuma shekara daya bayan nan ta fara a yakin kudancin kasar.

A shekarun 1940 Najeriya ta zamo wata babbar kasar dake samar da Kuza, Kolombite da kwal.

Sai dai kuma samun man fetur a shekarar 1956 yasa an tsayar da tono wadannan ma'adanan, hakanan kuma yakin basasar da aka yi yasa masana kan tonar ma'adanai suka fice daga kasar.

1. Kwal: A shekarar 1909 ne aka fara gano kwal a Najeriya a jihar Enugu dake kudu maso gabashin kasar, inda zuwa shekarar 1960 ake samun tan 565,681.

A iya cewa tun bayan yakin basasar da aka yi hakar kwal ta yi sanyi a Najeriya kuma har yanzu bata farfado ba.

2. Zinare: A shekarar 1913 ne aka fara hakar zinare a Najeriya inda ya kara bunkasa a shekarun 1930.

A garuruwan Maru, Anka, Malele, Tsohon Birnin Gwari-Kwaga, Gurmana, Bin Yauri, Okolom-Dogondaji da Iperindo dake kusa da jihar Kwara ne ake samun Zinare.

3. Kwalambite da Tantalite: Wadannan suma wasu ma'adanai ne da a aka fi sani da Coltan a nahiyar Afirka da ake amfani da su wajen sarrafa kayayyakin lataroni ko kayan wuta.

A jihar Nasarawa ne ake samun Coltan da ma wasu wurare a kudu maso gabashin Najeriya.

4. Bitumen: A shekarar 1900 aka fara gano ma'adanin Bitumen a Najeriya, aka kuma fara hakarsa a shekarar 1905.

Ana samun ma'adanin Bitumen a jihohin Legas, Ogun, Ondo, da Edo.

5. Tama da Karafa: Najeriya na da dinbin albarkatun Tama da karafa, sai dai mafi inganci shi ne wanda ake samu a wuraren Itakpe dake jahar Kogi.

A shekarar 1970 ne aka kafa kamfanin hakar tama da karafa dake jahar Kogi wato National Iron Ore Mining Company, domin samarwa da kamfanin sarrafa karafa na Ajakuta da na Aladja abin sarrafawa.

6. Makamashin Uraniyum: Ba tun yanzu bane aka gano Najeriya na da makamashin Uraniyum, sai dai a kwanannnan ne ma'aikatar binciken kasa da ma'adanai ta Burtaniya ta gano makamashin Uraniyum a jahohin Adamawa, Cross River, Taraba, Plateau, Bauchi, da kuma Kano.

Masaka

Tun kafin Najeriya ta samu 'yancin kanta a shekarar 1960 da ma gabanin samun man fetur, kasar ke da wasu masana'antu da ke samar mata kudaden shiga.

Wadannan masana'antu a wancan lokacin sun hada da masaka, wadanda ke daga cikin manyan masana'antun da kasar ke da su a baya.

A shekarar 1956 ne aka fara kafa masakar farko ta zamani a Najeriya a jihar Kaduna dake arewacin Najeriya, wannan kuwa baya rasa nasaba da irin yawan audugar da ake nomawa a arewacin kasar.

Najeriya ta kasance kasa ta 3 a Afirka a jerin kasashen dake da karfin masaku a shekarun 1970 da 1980.

A shekarar 1987, kasar na da masaku dake aiki 37, kuma tsakanin shekarun 1985 zuwa 1991 masana'antar ta habaka da kashi 67%, kuma tana samar da guraban aiki 25% a duk fadin kasar.

Sai dai kuma duk wannan ya zama tarihi a fannin masana'antu a Najeriya, biyo bayan wasu dalilai da suka hada da ka'idojin da kasashen da suka ci gaba suka gindayawa kasashe masu tasowa, na yawan kayayyakin sawar da zasu iya kaiwa kasashensu.

Bukatar man fetur da aka samu a kasuwannin duniya ya kara dauke hankali daga kan masaku zuwa wannan fanni, inda ko da yake har zuwa shekarun 1990 ba'a bar masaku ba amma dai ba'a basu muhimmancin da ake basu kafin wannan lokaci.