Jami'yyar gurguzun Koriya ta Arewa zata gudunar da babban taro

Image caption Shugaban kasar korea ta Arewa

Koriya ta Arewa ta bayyana cewa za ta gudanar da wani babban taro domin zabar sababbin shugabannin da za su jagoranci jam'iyyar gurguzun kasar, a ranar Talatar makon gobe.

A baya dai an samu labarin cewa za'a gudanar da wannan gagarumin taron da rabon da ayi irinsa tun 1980 ne a farkon watan Satumba.

Wakilin BBC ya ce sanarwar ta janyo hankalin masu bibiyar al'amuran Koriya ta Arewa wanda da dama ke ganin za'a yi amfani da taron ne wurin nada dan autan Kim Jong Il, mai suna Kim Jong-un, a matsayin magajinsa.

Sai dai kuma an rika rika yada jita jitar cewa an dage taron ne tun farko saboda matsalar ambaliyar ruwa ata afkawa kasar ko kuma rashin lafiyar da shugaban kasar ke fama da ita ta kara muni.