Rikicin Yankin Naija Delta

Image caption Gurbataccen muhalli sanadiyar hako danyen mai a yankin Niger Delta

Rikicin yankin Naija Delta ya samo asali ne tun kafin Najeriya ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Ingila, lokacin da kananan kabilu ke ta neman a raba su da manyan kabilu, wanda hakan ya sa gwamnatin mulkin mallaka ta kafa wata hukuma ta musamman domin duba bukatun kananan kabilun.

Misali, 'yan kabilar Ijaw a yankin Naija Deltan sun nuna rashin amincewarsu ga hade yankunan arewa da na kudanci.

Karin yawan man fetur din da aka samu a yankin Naija Delta a shekarun 1950 ya kara sa kabilun yankin tada kayar baya.

A shekarar 1966, masu fafutukar kwato yankin suka fara neman da a baiwa yankin Naija Delta 'yancin kai wanda Isaac Boro ya jagoranta.

Kodayake tsakanin watan Fabrairu zuwa Maris na shekarar 1966 gwamnati ta murkushe su, kuma tun wancan lokacin ba'a sake jin 'yan tawaye ba a yankin Naija Delta har sai lokacin da Ken Saro Wiwa shi ma wani mai fafutukar kwato 'yancin yankin Naija Deltan ya kaddamar da nasa tawayen.

A shekarar 1995 ne sojoji karkashin mulkin janar Sani Abacha suka kashe shi, bayan zargin da aka yi wa magoya bayansa da kashe wasu 'yan Ogoni.

Tun bayan wannan lokacin ne kuma ake ta samun tashe tashen hankula a yankin Naija Delta, inda masu fafutuka ke yin fito na fito da gwamnati da kuma sace mutane musamman ma'aikatan kamfanonin man petur suna garkuwa da su.

Image caption Masu ikirarin fafutukar neman yancin yankin Niger Delta

Daga cikin batutuwan da masu fafutukar kwato yankin Naija Delta ke kuka akai shi ne na rashin kulawar gwamnati wajen samar wa yankunansu ababen more rayuwa, duk kuwa da cewa sama da kashi 80 cikin 100 (80%) na arzikin kasar na fitowa ne daga yankin.

Har ila yau masu fafutukar na kokawa da gurbata muhallinsu da suka ce kamfanonin man na yi, abinda ke hana su samun tsaftataccen ruwan sha da ma yanayi mai kyau da kuma kashe albarkatun ruwan da suke da su.

A wannan karon kungiyoyin dake fafutukar sun lashi takobin hana hako mai a yankin, muddin dai gwamnati bata biya musu bukatunsu ba.

A ranar 13 ga watan Mayun shekara ta 2009 gwamnati ta kaddamar da yaki da su, inda ta tura sojoji yankin domin yakarsu.

A matsayin Najeriya na kasa ta 7 dake da arzikin man fetur a duniya, rikicin yankin Naija Delta a wannan lokacin ya yi matukar sanyawa an samu raguwa a man fetur din da kasar ke hakowa a kowace rana, inda ta yi asarar biliyoyin daloli daga kudaden shigar da take samu.

'Yan gwagwarmayar yankin Naija Deltan sun ci gaba da fafutuka har zuwa watan Agustan shekara ta 2009 lokacin da shugaba Umaru Musa 'Yar Aduwa ya yi musu tayin afuwa ga wadanda suka ajiye makamansu, tare da sama musu aikin yi.

Kuma a watan Yulin shekarar ne babbar kungiyar masu fafutukar kwato yankin Naija Deltan wato MEND ta bayar da sanarwar tsagaita wuta na kwanaki 60, domin ganin ko gwamnatin za ta cika alkawarinta.

Bayan da wa'adin kwanaki sittin din ya cika ba tare da ganin alamun cika alkawarin da gwamnati ta yi musu ba wasu kungiyoyin sun yi barazanar sake daukar makamai, ko da yake gwamnatin Dr Goodluck Jonathan ta yi alkawarin cika alkawarin da marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar Aduwa ya dauka domin gudun komawa yar gidan jiya.