Yawan jama'a a Najeriya

Image caption Najeriya na da yawan jama'a wajen sama da miliyan 140

Najeriya ita ce kasar da tafi kowace yawan jama'a a nahiyar Afrika, wanda kidayar da akayi a watan Maris na shekara ta 2006 ya nuna cewa yawan jama'ar ta ya haura miliyan 140, inda ta kasance kasa ta 9 a duniya dake da yawan jama'a, kuma ta ninka kasa mafi girma a Afirka wato Masar da yawan jama'a.

Bincike ya nuna cewa yawan jama'a a Najeriya na karuwa akai-akai, wanda a kidiyar da akayi a shekarar 1990 ya nuna kasar nada yawan jama'a miliyan 100 don haka ya karu da kashi 63% a wanda akayi a shekara ta 2006.

An kwashe shekaru 15 kafin kidayar da akayi a shekara ta 2006, ko dayake kamar kowace kidaya da akai a Najeriyar, in banda wadda aka gudanar a shekarar 1963 da jama'a sukayi na'am da ita, wannan ma jama'a da dama a sassa daban daban na kasar sun nuna shakkunsu game da sakamakonta, wanda ya nuna arewa tafi sauran yankunan kasar yawan jama'a.

Jihar Kano ita ce tafi kowace yawan jama'a da mutane miliyan 9.4 inda jahar Lagas ke binta da miliyan 9.

Kamar kowace kidaya da aka gudanar a Najeriya, sauran sassan kasar sun yi zargin an karawa arewa yawan jama'arta domin a bata kaso mafi tsoka daga aljihun gwamnati.

Wani batu da ke da muhimmamci game da kidayar shi ne batun shugabanci da raba madafan iko a tsakanin sassan kasar, inda bangaren da yafi yawa shi zaifi samun mukamai ko kujeru a gwamnati.

Wannan yasa a duk sanda aka gudanar da kidayar jama'a 'yan kudu ke zargin an rage musu yawan jama'arsu.

Kidayar jama'a da aka gudanar a Najeriya a shekara ta 2006 ta nuna cewa yawan maza a kasar ya kai miliyan 71, 709,859 yayin da su kuma mata ke miliyan 68,293,683 kuma hakan ya nuna cewa maza sun fi mata yawa.

Duk da irin arzikin da Allah yaiwa Najeriya akasarin jama'arta na rayuwa kan kasa da dala daya a rana, yayinda da yawansu ke zaune a karkara.

Wannan yasa a kowace shekara ana samun mutanan dake kaura daga kauyuka zuwa manyan birane domin samun saukin rayuwa.