Rikice-Rikicen kabilanci da addini a Najeriya

Image caption Sojoji na tabbatar da zaman lafiya a Jos

Tun bayan samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka, Najeriya ta sha fama rikice rikicen addini da na kabilanci harma da na siyasa a lokuta daban-daban.

Rikice-rikicen dai sun haifar da asarar rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa.

A farkon shekarar 1980 ne aka yi rikicin Maitatsine a jihar Kano, wanda daga bisani ya bazu zuwa Yola, Maiduguri, Bauchi da Gombe, inda aka yi hasarar rayukan dubban mutane da suka hada musulmai da kiristoci.

Bayaga yakin basasar da Najeriya ta fuskanta a shekarun 1967 zuwa 1970 wanda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa, ko da yake wannan za a iya cewa rikicin kabilanci ne, rikicin Maitastine shi ne rikicin addini na farko mafi muni da kasar ta fuskanta a jamhuriya ta biyu karkashin mulkin Alhaji Shehu Aliyu Shagari.

Tun daga wancan lokacin da aka yi rikicin Maitatsine a arewacin Najeriya, an yi ta samun rikice rikicen addini da na kabilanci daban-daban, kama daga arewaci zuwa kudanci zuwa gabashin kasar.

Rikice-rikicenda suka fi muni sun hada da rikicin Zangon Kataf a jihar Kaduna a shekarar 1992 tsakanin Hausawa da Katafawa, wanda daga bisani ya rikide ya koma na addini.

A wannan rikicin shi ma an yi asarar rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa.

Sai kuma rikicin Shagamu a jihar Ogun a watan Yulin shekarar 1999 tsakanin Yarabawa da Hausawa, biyo bayan kisan wata mace Bahaushiya da wata kungiya mai suna kungiyar Oro ta yi, inda suka ce ta keta ka'idarsu.

Kashe-kashen da aka yi wa Hausawa a Shagamu ya sa a Kano ma matasa sun dau fansa kan Yarabawan dake zaune a can.

A watan Nuwamban shekarar 1999, rikicin kabilanci ya barke a unguwar Ajegunle a jihar Legas tsakanin kungiyarOPC da ta matasan kabilar Ijaw.

Bayan kwantar da wannan rikicin a watan Disambar wannan shekarar, an sake samun wani rikicin kabilancin a kasuwar Mile 12, tsakanin kungiyar OPC da Hausawa, bisa dalilan shugabancin kungiyar masu sayar da doya a kasuwar wato Shukura Yam Sellers Association, wadda kusan Hausawa ne ke rike da shugabancinta, inda aka yi asarar rayuka sama da dari biyu tare da kone kasuwar kurmus.

Bullo da tsarin shari'ar musulunci a wasu jihohin arewacin kasar shi ne ya haddasa rikicin addini a jihar Kaduna a watan Fabrairun shekara ta 2000, inda nan ma aka yi rikici tsakanin musulmai da mabiya addinin kirista wadanda suka nuna rashin amincewarsu ga amfani da shari'ar musulunci a jihar.

Rikicin wanda ya bazu zuwa garuruwan Kachiya, Zaria da sauranzu ya hadasa asarar daruruwan rayuka da dukuyoyi masu dimbin yawa.

Bayan wannan rikicin na Kaduna an samu makamancinsa a jihohin Sokoto da Borno musamman ma a garin Damboa na jahar Borno.

An fara samun rikici a Jos tun daga shekara ta 2001, wanda asalinsa na siyasa ne tsakanin 'yan asalin yankin Pilato da kuma Hausa/Fulani dake zaune a can, kafin daga bisani ya rikide ya koma na addini da kabilanci, kuma ya kasancedaya daga cikin manyan rikice-rikicen da aka samu a Najeriya.

Rikincin Jos na faruwa ne tsakanin Hausa/Fulani musulmai da kuma ‘yan yankin na Pilato wadanda akasarinsu mabiya addinin kirista ne.

Bangarorin biyu na takaddama ne kan ko suwaye 'yan asalin jihar da kuma wadanda za su yi shugabanci.

Kan haka ne wasu ke ganin baya ga kabilanci da addini, rikicin jos na da alaka da siyasa.

An samu asarar rayuka da ma dukiyoyi masu dimbin yawa tun daga lokacin da aka fara zaman doya da manja a garin, wato daga shekara ta 2001 zuwa ta 2010.

Rikice-rikicenda aka yi ta yi a Jos a shekarun baya-bayan nan kan bazu zuwa jihohin dake makwabtaka da ita kamar Gombe da Bauchi.

Ana cikin wannan yanayi ne kuma wani rikicin ya balle a arewacin Najeriyar, wato rikicin Boko Haram wanda ya auku a watan Yulin shekara ta 2009, inda wasu matasa na wata kungiyar musulunci karkashin jagorancin mallam Muhammad Yusuf dake adawa da ilimin boko suka kaddamar da yaki kan jami'an tsaro da ofisoshinsu a garin Maiduguri na jahar Borno.

Domin dakile ayyukan kungiyar, gwamnatin tarayya da ta jihar Borno sun baiwa jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da sojoji izinin bude wuta kan 'yan kungiyar ta Boko Haram.

A bata kashin da aka yi tsakanin 'yan kungiyar da jami'an tsaro, an kashe da dama daga cikin 'yan kungiyar tare da kama wasunsu.

Kungiyar ta kwashe kwanaki tana gumurzu da jami'an tsaro a jahar ta Borno, inda wasu suka ce wasunsu sun ketara zuwa jihar Gombe.

A ranar Talata 7 ga watan Satumbar shekarar 2010, wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, sun kai hari gidan yari na jihar Bauchi inda suka balla shi suka kuma kubutar da wasu magoya bayansu da ake tsare dasu a ciki.