Harkar sufuri a Najeriya

Shekaru hamsin kenan da Najeriya ta samu 'yanci kanta daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya, amma har yanzu akwai sauran tafiya ta wajen ci gaba musamman idan aka duba yadda gwamnatin kasar ke cewa zata shiga jerin kasashe 20 din da ke da karfin tattalin arziki da masana'antu nan da shekara ta 2020.

Domin kuwa akwai jan aiki a gabanta ta fannoni da dama, wanda harkar sufuri na daga cikin kalubalan da kasar ke fuskanta.

A matsayinta na kasar da tafi yawan jama' a a nahiyar Afirka kuma ke harkokin kasuwanci iri daban-daban yasa tilasne ta samu ingantaccen tsarin sufuri da zirga-zirgar jama'a.

Gabanin samun 'yancin kan Najeria a shekarar 1960, jama'a na da hanyoyin da suke zirga-zirga a ciki da wajen kasar da suka hada da ta ruwa da kasa.

A wancan lokacin kasar na da tashoshin jiragen ruwa a garuruwa kamar Lagas, Patakwal da Calabar. Sai kuma ta kasa, inda ake amfani da dawakai da jakuna musamman a arewacin kasar.

Da zuwan turawa sun yi kokarin gyara hanyar sufurin da dama da suka tarar wato ta ruwa da kasa, suka kuma gina layin dogo wato suka kawo hanyar sufuri ta jirgin kasa domin kawo saukin safarar kayayyaki tsakanin wannan bangare na kasar zuwa wancan.

Bayan da Najeriya ta samu 'yancin kai gwamnatin kasar karkashin jagorancin Sir Abubakar Tafawa Balewa tayi kokarin gina wasu hanyoyin sufurin da suka hada da tashoshin ruwa da jirgin kasa, da ma samar da titunan mota a wasu wuraren da daman can ba bu.

Hakan kuma a lokacin da kasar ta samu bunkasar tattalin arziki a shekarun 1970 ta hanyar man petur, gwamnatin sojin wannan lokacin ta ware kashi 20% na kudaden shigar da ta samu domin bunkasa hanyoyin sufurin kasar da suka hada da ta ruwa, ta jirgin kasa, ta jirgin sama da hanyar mota.

1. Hanyar Sufuri ta Ruwa: Najeriya kasa ce da ke da mashigan ruwa ta bangarorin kudu da yammacin kasar, kamar Lagas da Patakwal da ma Calabar, inda tun kafin samun 'yancin kan kasar ake da tashoshin jiragen ruwa da ake harkokin kasuwanci a wuraren, musamman safarar bayi a lokacin cinikin bayi.

Daga bisani kuma an gina wasu tashoshin jiragen ruwan a a yankin Niger Delta kamar na Warri, Sapele, Koko, Burutu, Bonny da Alesa.

Da zuwan wasu hanyoyin sufurin yanzu haka ba sosai ake amfani da hanyar sufuri ta ruwa ba in banda shigo da kayayyaki, abinda yasa masu lura da al'amura ke ganin gwamnati bata maida hankali wajen inganta tashoshin jiragen ruwan kasar.

2. Hanyar Sufuri ta Jirgin Kasa: Tun kafin Najeriya ta samu 'yancin kanta, turawan mulkin mallaka suka kawo hanyar sufuri ta jiragen kasa domin saukaka safarar kayayyaki daga wani bangaren kasar zuwa wani, musamman ma daga arewaci inda ba tashar jirgin ruwa zuwa kudanci ko yammacin kasar domin fitar da su zuwa kashen waje.

Sai dai kuma a iya cewa tun bayan da turawa suka mika ragamar mulkin Najeriya ga 'yan kasar ba wani ci gaban a zo a gani da aka samu a fannin sufurin jiragen kasa, yawanci ma na ganin akasin hakan aka samu.

Akwai manyan layukan dogo biyu a kasar dake da tsawon kilo mita 3,505, wadda ta taso daga Iddo a jahar Lagas zuwa Nguru a jahar Yobe a arewacin kasar.

Daya layin dogon kuma ya taso ne daga Patakwal zuwa wasu jahohin arewacin kasar har Maiduguri zuwa Kauran Namoda. Rashin kulawar sufurin jirgin kasa na shekara da shekaru yasa jama'a da dama a Najeriya kusan mantawa da ita, yayinda 'yan injinan jiragen da suka rage a kasar suka zama tsohon yayi.

A shekarar 1999 gwamnatin Obasanjo ta so farfado da harkar sufurin jiragen kasa, inda ta bada kwagilar gina wasu layin dogon tare da shigo da sabbin jiragen kasan na zamani, kuma wannan ma na daga cikin ayyukan da marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua yace zai bunkasa.

Sai dai kuma wasu na ganin batun cin hanci da rashawa yasa shirin ya salwanta.

Don haka masu iya magana kance da rashin uwa akanyi uwar daki, rashin jirgin kasa yasa 'yan Najeriya komawa ga mota da sauran ababen hawa na kasa.

3. Hanyar Sufuri ta kasa: Shekaru gabanin samun 'yancin kanta a shekarar 1960, Najeriya na da hanyoyin sufuri da jama'arta ke amfani domin zirga zirga daga wannan bangare zuwa wani, musamman ma daga kauyuka zuwa birane domin kasuwanci, wadanda suka hada da Dawakai, Jakuna, Mota da dai sauransu.

Tun a wannan lokacin akwai hayoyin da kowanne ke amfani da shi.

A shekara 1914 turawan mukin mallaka suka gina wasu tituna da ke da tsawon kilo mita 3,200 kuma ya zuwa shekarar 1960, lokacin da Najeriya ta samu 'yancin kanta, kasar na da tituna dake da tsawon kilo mita 66,000 wadanda suka hada wasu kauyuka da manyan birane dama sauran yankunan kasar.

Kuma a yanzu haka tsawon titunan da ake da su a kasar ya kai kimanin kilo mita 200,000 kuma daga cikin wadannan titunan iya tsawon kilo minta 50,000 ne kadai ke da kwalta .

Rashin kyan tituna a Najeriya na daga cikin abubuwan dake kawo mata koma bayan tattalin arzuki.

Gwamnatocin baya sun sha fidda kudi domin gyara titunan da ake da su a kasar wadanda ke cin rayukan daruruwan mutane a kullum.

Kamar yadda al'ummar Najeriya ke karuwa bayan kowace kidaya haka nan ma ake samun karin ababen hawan da ake shigowa da su cikin kasar, abinda ke janyo cunkoson ababen hawa akan titunan musamman ma a manyan biranen kasar kamar Kano, Lagas, Patakwal da sauransu.

Matsalar cin hanci na taka rawar gani wajen karkatar da kudaden da gwamnatocin kama daga na kananan hukumomi zuwa na jahohi har zuwa na gwamnatin tarayya, domin samar da kyawawan tituna a kasar. Kuma har sai an kawar da da ire-iren wadannan matsaloli kafin a samu nasarar samun ingantattun tituna ko hanyoyi a Najeriya.

4. Hanyar Sufuri ta Jiragen Sama: A iya cewa an samu ci gaba matuka ta hanyar sufurin jiragen sama tun daga shekarun 1920 kawo yanzu.

A shekarun 1970 zuwa 1980 aka gina filayen jiragen sama a jahohin kasar da dama, wato a lokacin da aka samu bunkasar tattalin arzuki ta hanyar man petur.

A shekara ta 2001 Najeriya na da kimanin filayen jiragen sama 70 daga cikinsu 36 ne ke shafe da kwalta. A filayen jiragen sama na Murtala Muhammed International Airport Lagas, Aminu Kano International Airport Kano, Nmandi Azikiwe International Airport Abuja da kuma na Patakwal ne jiragen kasashen waje ke sauka da tashi.

A shekarar 1961 ne kamfanin jiragen sama na Nigerian Airways ya zama mallakar gwamnatin tarayya wanda yake aiki a ciki da wajen kasar.

A farkon wannan karnin harkar sufurin jiragen sama ta yi ta haduwa da haddura a Najeriya, abinda masana ke ganin rashin kyawawan jirage da kwararru da ma kayan aiki ne ke haddasa ire iren wadannan haddura.