Majalisar Dinkin Duniya na taro kan Muradun Karni

Babban taron Majalisar Dinkin Duniya
Image caption Babban taron Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya tana yin wani taro a birnin New York na Amurka.

Makasudin taron shi ne yin nazari a kan irin nasarori da kuma matsalolin da aka samu, wajen cimma muradun karni nan da shekara ta 2015.

Gurorin da ake cimmawar, galibi sun shafi rage talauci ne.

Galilbinsu babu alamar za a cimma su nan shekarar ta 2015, illa wanda ya shafi rage tsananin talauci da kamar rabi, wanda galibin jama'a ke fama da shi.