Harkar Illimi a Najeriya

Image caption Daliban illimin boko a Najeriya

Ilimin Arabiya:

Nijeriya kasa ce da ke da mabiya addinai daban daban, manyan a cikinsu Musulunci da Kiristiyaniti wadanda suka shigo kasar shekaru aru-aru kafin zuwan turawan mulkin mallaka.

Kuma tun daga wannan lokaci ake samun hanyoyin ilmantar da jama'a.

Alal misali tun karni na 14, lokacin da musulunci ya shigo arewacin kasar ake koyar da jama'a harshen larabci ta yadda zasu iya karatun al-qur'ani da ma karin ilimi game da addinin, kuma an kara fadada tare da karfafa karatun larabci a lokacin jihadin Sheikh Usman Dan Fodio a sauran kasashen Hausa.

Wannan ya nuna cewa Ilimin arabiya ya riga ilmin boko ko na zamani shigowa Najeriya, wanda aka fara koyar da shi a karni na 19.

A shekarar 1934 a zamanin Sarki Abdullahi Bayero na Kano ne aka fara gina makarantar koyan harshen larabci a Kano, inda ake koyar da shari'ar musulunci, kuma bayan Arabiyya ake koyar da Turanci da Lissafi.

Makarantar ta bunkasa so sai, inda cikin kankanin lokaci aka mai da ita ta zama Kwalejin Bayero, wadda ta zama wani bangare na jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya, daga bisani kuma ta zama jami'ar Bayero ta Kano.

An giggina makarantu da dama a arewacin Najeriya wadanda suka fi baiwa harshen Larabci karfi , kuma hakan ya kasance wata matsala ga daliban dake zuwa wadannan makarantun, ganin cewa ba'a amfani da larabci a yawancin bangarorin kasar.

Ilimin Boko:

Da zuwan kungiyoyin mishan Najeriya a tsakanin shekarar 1842 zuwa 1914 ne ilimin boko ko kuma na zamani ya shigo kasar, yayin da a tsakanin wadannan shekarun kimanin kungiyoyin mishan-mishan 10 suka shigo suna ayyuka daban daban da suka hada da ilmantar da jama'a wanda suka baiwa karfi sosai.

Tun daga wannan lokacin aka giggina makarantu ana daukar jama'a musamman yara domin basu ilimin boko.

Baya ga darrusa 4 da ake koyarwa a makarantun, wadanda suka hada da karatu, rubutu lissafi da kuma addininsu wato kiristiyaniti, akan horas dasu ta yadda zasu samu aikin yi kamar koyarwa, wa'azi a coci-coci akawu da tafinta.

A shekarar 1857 ne aka gina makarantar CMS Grammar School dake Lagas.

Ilimin boko bai samu karbuwa a arewacin Najeriya ba sosai a wancan lokacin, saboda ana tsoran kada ya gurbata addinin musulunci.

An kiyasce cewa a shekarar 1914 an samu makarantun Arabiya kimanin 25,000 a duk fadin arewacin Najeriya, wanda hakanne ya jawo rashin karbuwar ilimin boko ko kuma na zamani a yankin, ko da yake kungiyoyin mishan-mishan din sun samu karbuwa a wasu sassan arewacin kasar, inda suka gina makarantunsu.

A tsakanin shekarar 1882 zuwa 1950 ne shugabannin yankunan kasar suka fito da ka'idojin yadda za'a riki koyar da jama'arsu wanda da ba bu, kuma a tsakanin shekarar 1952 zuwa 1960 dukkanin yankunan uku suka shimfida sabbin dokokin tsarin koyarwa a yankunansu, wanda aka fara gwadawa da shirin ilimin baidaya na piramari a yammacin kasar a shekarar 1955, a gabashin kasar kuma 1957.

A shekarar 1952 ne aka kafa hukumar shirya jarabbawa ta kasashen yammacin Afirka wato WAEC.

Bayan da Najeriya ta samu 'yancin kanta a shekarar 1960 gwamnatin tarayya ta bude jami'o'i 5 wadanda suka hadar da:

Jami'ar Nsukka(1960)

Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya (1962)

Jami'ar Ile-Ife (1962)

Jami'ar Lagas (1962)

Jami'ar Ibadan wadda aka fara kafa ta a shekarar 1948

Jami'ar Benin (1972)

Dukka wadannan da nufin bunkasa ilimi tare da magance wasu matsaloli da gwamnatin tun a wancan lokaci ta fara hanga.

Baya ga wadannan jami'o'in, gwamnatin ta giggina wasu manyan makarantun da nufin samar da ilimi a wasu bangarorin kamar fasaha da kere kere.

A lokacin da Najeriya ta samu bunkasar tattalin arziki ta hanyar man petur, gwamnatin tarayya ta bullo da shirin ilimin bai daya na bada ilimi kyauta a makarantun piramare.

Sai dai kuma ba'a je ko ina ba shirin ya wargaje saboda rashin kyakyawan shiri da isassun kudade.

A shekarar 1999 ne gwamnatin tarayyar ta sake kaddamar da wani shirin bada ilimin bai daya da nufin bunkasa ilimin da akai na farkon.

Sai dai kuma har yanzu ba'a kai ga cimma burin bunkasa ilimi a kasar ba saboda wasu matsaloli ko dalilai da kasar ke fuskanta.

Matsalolin da Ilimi ke fuskanta a Najeriya:

1. Talauci: Nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati tun daga tarayya har zuwa kananan hukumomi, na ta baiwa al'ummarta ilimi akalla na piramare, sai dai kuma ba ko ina ne gwamnatin ke sauke wannan nauyi ba, musamman ma a yankunan karkara, inda a wurare da dama babu koda dakin karatu daya, inda aka samu kuma imma ba malamai ko kuma kayayyakin aiki.

A irin halin da kasar ke ciki na tattalin arziki jama'a da dama na cikin talauci ne don haka baza su iya daukar dawainiyar karatun 'ya'yansu ba.

2. Tattalin Arziki: Baya ga talauci da ke kawo koma bayan ilimi a Najeriya, musamman ma dai a arewacin kasar, batun tattalin arzuki da zafin nema da dogaro da kai ya kasance wata matsalar da fannin ilimi ke fuskanta a Najeriya, musamman ma dai a gabashin kasar.

A wannan yankin ba safai 'ya 'ya maza ke kammala karatunsu na piramare ba, inda suka fi maida hankali wajen kasuwanci, 'ya'ya mata ne kadai ke kaiwa har jami'a.

Wannan kuwa ya samo asali ne tun lokacin yakin basasar da akai a kasar, lokacin da tattalin arzikin yankin ya shiga halin ni'yasu.

Can kuma a arewacin kasar matsalar rashi ko talauci ke sa iyaye gwammacewa su dorawa 'ya'yansu talla a madadin turasu makaranta, wannan kuwa ba ga mata ba, ba ga maza ba.

3. Al'ada ko Addini: Batun al'ada ko addini wata babbar matsala ce dake fuskantar fannin ilimi a Najeriya musamman ma a arewacin kasar.

Wannan kuwa ya hada da yiwa 'ya'ya mata auren wuri, abin da yasa ake samun 'ya 'ya maza na zuwa makaranta fiye da mata. Yawancin jama'a a yankin na kyamatar cudanyar maza da mata a wuri guda.

4. Malamai da kayan aiki: Babbar matsalar da yanzu haka fannin ilimi ke fuskanta a Najeriya ita ce ta rashin kayan aiki wanda ya kamata gwamnati ta samar a makarantu, kuma wannan shine babban abin da ke jawo karancin malamai a makarantun, kama daga piramare har zuwa jami'o'i.

Baya ga rashin kayan aikin akwai kuma rashin biyan bukatun malaman da gwamnatin ke yi, wanda hakan ne ke sa kwararrun malaman makaranta, musamman daga shekarun 1980 zuwa 1990, lokacin da gwamnati ta fito da shirinta na tsuke bakin aljihu wato SAP barin kasar zuwa wasu kasashen waje.

A wannan lokacin malaman kan koma Ingila, Amurka, Afirka ta Kudu da dai sauransu.

Kowace gwamnati kan zo da nata shirin kawo gyara ga fannin ilimi a Najeriya, sai dai kuma har ya zuwa wannan karnin ba'a samu wadda ta yi nasara ba, inda a kullum sai kara tabarbarewa yake.