Janar Konate ya bukaci a gudanar da zabe zagaye na biyu a Guinea

Shugaban mulkin sojin kasar Guinea, General Sekouba Konate, ya bukaci a fitar da sabon lokacin gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.

Janar Konate ya bayyana hakan ne a wani taro da yayi da 'yan takarar shugabancin kasar guda biyu, da jami'an gwamnati da hukumar zaben kasar, inda ya ce ba zai lamuncewa a sake dage zaben ba.

Dama dai, kamata yayi a gudanar da zaben a ranar lahadin ta gabata, to amma aka soke, bayan kwana da kwanakin da aka yi ana fadace-fadace tsakanin magoya bayan 'yan takaran.

Janar Konate ya ce, burinsa ya cika, kuma yana da kwarin gwiwar mika mulkin kasar a hannun farar hula.