Firai Ministan Somalia ya yi murabus

Omar Abdirashid Ali Sharmarke
Image caption Omar Abdirashid Ali Sharmarke

Firai Ministan Somalia Omar Abdirashid Ali Sharmarke ya ajiye aikinsa, a yayin da ake takkadama game da shugabancin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya dai na goyon bayan gwamnatin Shugaban kasar Sheikh Sharif Ahmed wanda ke yakan kungiyar addinin Islama wato Al-Shabab da ke neman karbe madafin iko a Mogadishu.

Mista Sharmarke ya fuskanci matsin lamba a watannin da su ka gabata domin ya yi murabus.

A watan Mayun da ta gabata ne Firayim Ministan ya ki amincewa da kuri'ar da Majalisar kasar ta kada domin neman ya sauka daga mukaminsa.

Shugaban kasar da Firai Ministan kasar dai na hannun riga da juna game da kudurin sabon kudin tsarin mulkin kasar.