Ana tuhumar shugaban bankin fadar Vatican

Masu gabatar da kara sun fara tuhumar shugaban bankin Fadar Vatican wato Ettore Gotti Tedeschi, wanda ake gudanar da bincike kansa bisa zargin keta dokokin hada-hadar kudi na yin sama da fadi da wasu kudade.

Haka kuma sun kwace fiye da dala million 30 na bankin. Mr Gotti Tedeschi da wani manajan bankin, na fuskantar zargin keta dokar da ta tilastawa bankuna su bada bayani kan hada-hadar kudadensu.

A baya dai bankin ya fuskanci wani babban rikici a shekarar 1980, lokacinda bankin ya haddasa rushewar wani bankin yan kasuwan kasar Italiya wato Banco Ambrosiano.