Matsalar ruwan sha a Najeriya

Image caption Jama'a na jerin gwano domin neman ruwan sha

Ruwa aka ce shi ne ginshikin rayuwa, don haka samar da tsabtatatcen ruwan sha ga jama'a wani nauyi ne da ya rataya a wuyan kowace gwamnati.

Gabanin shekarar 1960, lokacin da Najeriya ta samu 'yancin kanta daga turawan mulkin mallaka na Ingila, 'yan kasuwa ne ke tafiyar da harkar samar da ruwansha da ma na amfanin jama'ar kasar.

Har sai a shekarar 1962 zuwa 1968 ne gwamnatin ta fara shiga harkar samar da ruwa, a lokacin da ta kafa hukumar raya kogin Naija da ta raya tafkin Chadi, wadanda aka dorawa alhakin zana taswirar wuraren da ake samun ruwan da za'a yi amfani da shi wajen noma, kamun kifi, kiwo da ma zirga-zirgar jama'a, sai kuma hukumomin samar da ruwan sha a manyan-manyan birane, inda aka yi watsi da yankunan karkara.

Mummunan farin da aka yi a farkon shekarun 1970 ya kara ankarad da gwamnatin tarayya game da samarwa da jama'arta wadataccen ruwan sha da na noma da kamun kifi da dai sauransu.

Don haka ne ma ta kafa wasu hukumomin da suka hada da ma'aikatar ruwa, karin wasu hukumomin raya koguna da suka hada da ta kogin Rima na Sokoto, sai kuma cibiyar kula da arbarkatun ruwa ta kasa.

Yayin da ma'aikatar ruwa ke da alhakin tsara ayyuka da bada shawarwari, ita kuma cibiyar kula da albarkatun ruwan na horas da ma'aikatansu ne da kuma gudanar da bincike-bincike. Su kuma hukumomin raya kogunan na samar da ruwan sha ne da na noma da kiwo.

An samu karin wadataccen ruwan sha a lokacin da Najeriya ta kaddamar da wani shiri a sherakar 1980, lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke shirye-shiryen bikin ranar cika shekaru dari na samar da tsabtataccen ruwan sha da muhalli ta duniya.

Makasudin wannan shiri shi ne na samar da ruwan sha ga kowa kafin nan zuwa shekarar 1990, wato kimanin lita 120 na amfanin gida a rana.

Gabanin wannan shirin dai kashi 22% na al'ummar yankunan karkara ne ke samun tsabtataccen ruwan sha, yayin da kashi 55% na jama'ar dake zaune a birane ke samun tsabatataccen ruwan sha.

Wato ya zuwa shekarar 1986 kowane mazaunin karkara na samun lita 25 na tsabtataccen ruwan sha, yayin da na birni ke samun lita 60 a rana. 'Yan shekaru bayan wannan shiri, batun samar da ruwa ga jama'a ya fara shiga wani hali, hakan kuwa ya faru ne bisa wasu dililai da suka hada da:

1. Rashin alkaluman da za'a yi amfani da su wajen samar da tsare-tsare daga tushe, wadanda a lokuta da dama ba'a ba su wani muhimmanci ko ma ai watsi da su.

Don haka da wuya a samu sahihan alkaluman da za su taimaka wajen tantacewa, tsarawa, da kula da kayayykin da ake amfani dasu wajen samar da ruwan shan. Kuma rashin ire-iren wadannan alkaluman kan gurgunta ayyukan samar da ruwan, alal misali madatsar ruwa ta Bagauda wanda a iya cewa kwalliya bata biya kudin sabulu ba ganin irin makudan kudaden da gwamnati ke kashewa.

2. Ambaliyar Ruwa da Zaizaiyar kasa, suma wasu manyan matsaloli ne dake kawo cikas wajen samar da tsabtataccen ruwan sha ga al'umma, a Najeriya. Matsalar ambaliyar ruwa kan kai ga asarar kasar noma da kuma lalata kayayyakin da ake amfani dasu wajen samarwa da tura ruwan ga jama'a.

3. Karancin Ma'aikata: Wannan wata babbar matsala ce da ake fuskanta wajen samarwa da jama'a tsabtataccen ruwan sha musamman kwararru a fannin.

Ana rarraba 'yan kalilan din da ake da su a kasar ne zuwa bangarorin gine gine, ayyuka da kuma kula da sa ido kan ayyukan da ake yi.

Don haka muddin gwamnatin Najeriya na son shawo kan matsalar karancin ruwa ga al'ummarta, tilas ne ta tashi tsaye wajen samar da karin kwararrun ma'aikata tare da horas dasu game da aikin.

4. Karancin Kudade: Rashin kudaden tafiyar da ayyukan samar da tsabtataccen ruwan sha dama na sauran amfanin noma da kiwo wata babbar matsala ce a Najeriya.

Gwamnati ce ke daukar dawainiyar tafiyar da yawancin ayyukan samar da ruwa a kasar, kuma rashin isassun kudaden da ta ke fuskanta na kawo tafiyar hawainiyar ayyukan samar da ruwan.

Kudaden da gwamnatin tarayya ke warewa bangaren ruwa ya yi kasa, yayin da gwamnatocin jahohi ke ware kashi 20% zuwa 30% na kasafin kudinsu ga bangaren samar da ruwa a jahohinsu.

Wannan ke sa ake gaza kammala wasu aikace-aikacen samar da ruwa wadanda kuma suka lalace ba'a iya gyarasu.

Alal misali gwamnati ta gaza kammala ayyukan gina fadamun noman rani a wurare da dama a duk fadin kasar, abinda ke taimakawa wajen karancin abinci da kuma asarar kudaden shiga a kasar.

Don haka karancin tsabtataccen ruwan sha a Najeriya na ci gaba da kasancewa wata babbar annoba birni da kauye, lamarin da ya sake dawo da harkar samar da ruwan sha ga hannun 'yan kasuwa, da ke giggina rijiyoyin birtsatse suna saidawa jama'a ruwan da za su yi amfani dashi, wuraren da ba rijiyoyin birtsatsen kuma jama'a kan dogara ne kawai ga kowane irin ruwa suke da shi a wajen su koda kuwa ba tsabtatacce bane.

Wannan ne kuma ke kawo cutukan da ake samu ta ruwa kamar kwalara wato amai da gudawa.