Takaitaccen tarihin Janar Abdussalam Abubakar

Image caption Janar Abdulsalam Abubakar

Ranar 13 ga watan Yunin shekarar 1942 ne aka haifi janar Abdussalam Abubakar mai ritaya a garin Minna na jahar Naija.

Yayi karatun Firamarinsa a makarantar Native Authority a garin Minna, ya kuma yi karatun sakadiransa a makarantar Provincial Secondary School dake Bida da ga karshe kuma yaje makarantar Technical Institute, daka Kaduna, bayan wannan ne kuma ya shiga aikin soji.

Janar Abdussalam ya jagoranci dakarun sojin Najeriya a Labanon kuma daga bisani ya sa mu mukamin babban hafsan tsaro.

Janar Abussalam na da mace daya Mai sharia Fati da 'ya 'ya shida.