Mu ke gudanar da hare hare a Maiduguri-inji kungiyar Boko Haram

Image caption Shugaban kungiyar Boko haram

A karon farko kungiyar boko haram ta tabbartawa BBC cewa su keda alhakin kai jerin hare harea birnin Maiduguri.

Wani almajirin shugaban kungiyar wanda bai amince a fadi sunan sa ba ya ce su da gwamnatin gwamna Ali Modu Shariff suke fada, akan haka jama'a su kwantar da hankalinsu.

Ya kuma ce sune suka kai hari a wani gidan yari da ke jihar Bauchi a kwanakin baya.

A watan Yulin da ya gabata ne aka fara samun jerin hare-hare da kashe-kashen wasu jami'an yan sanda da masu unguwanni a birnin Maiduguri da wasu yan bindiga ke aikatawa.

Wannan bayanai nasu kuwa yazo dai dai lokacin da wasu yan bindigar suka sake kai wani hari jiya da rana a unguwar Gwaidamgari dake bayan tsohuwar Helkwatar ta Boko Haram suka sakarwa wasu mutane wuta inda mutum guda ya rasu.