An sace 'ya'yan shugaban hukumar Alhazai ta Filato

Rahotanni daga Jihar Filaton Nijeriya na nuni da cewa an sace yaran Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Filaton, Alhaji Auwalu Shehu Dan-Kurma su uku.

Yaran su uku da direbansu mai suna Muhammad Sani, sun yi batan dabo ne yayin da direban ke tuka su zuwa makarantar Plateau Private da ke cikin garin Jos a jiya.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Filato ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma ta ce suna tattaunawa da masu garkuwar wadanda ke bukatar a ba su miliyoyin Naira a matsayin kudin fansa.

Sai dai kuma rundunar 'yan sandan ta ce tana zargin hannun direban yaran a wannan sata.