Takaitaccen tarihin Shugaba Goodluck Jonathan

Image caption Shugaba Goodluck Ebele Jonathan

An haifi Dr. Goodluck Ebele Jonathan ranar 20 ga watan Nuwambar shekarar 1957 a garin Otueke na karamar hukumar Ogbia dake a wancan lokacin yankin gabashin Najeriya, yanzu kuma yake jihar Bayelsa.

Iyayensa na sassaka jirgin kwale kwale ne.

Yayi karatun digirinsa na farko a fannin ilimin dabbobi.

Ya kuma yi digirinsa na biyu a fannin ilimin halittun ruwa.

Ya samu digirin digirgir a fannin ilimin dabbobi a jami'ar Patakwal.

Bayan da ya samu digirinsa na farko ya yi aiki a matsayin sipeton dake sa ido kan yadda malamai suke gudanar da ayyukansu, malamin jami'a da kuma jami'in dake sa ido kan kare muhalli, aikin da yake har zuwa lokacin da ya shiga siyasa.

A shekarar 1998 ne Dr. Goodluck Jonathan ya fara shiga al'amuran siyasa, inda ya shiga jam'iyyar PDP.

Ya zama mataimakin gwamnan jihar Bayelsa a shekarar 1999 bayan da Diepreye Alamieyesegha ya lashe zaben gwamnan jihar karkashin tutar jam'iyyar PDP.

Dr Goodlck Jonathan ya zamo gwamnan jihar Bayelsa bayan da majalisar dokokin jihar ta tsige Alamieyesegha bisa zargin kokarin hallata kudin haram a Burtaniya da kuma almundahana da dukiyar jama'a.

A shekara ta 2006 an zabi Dr. Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa, kuma bayan zaben da aka yi a shekara ta 2007 an rantsar da shi a matsayin mataimakin shugaba Umaru Musa 'Yar Adua.

Kamar ubangidansa Dr. Goodluck ya bayyana dukkan dukiyar da ya mallaka daga lokacin da ya hau kan mulki.

An rantsar da Goodluck Jonathan a matsayin mukaddashin shugaban Najeriya sakamakon rashin lafiyar da shugaban Najeriya na lokacin Umaru Musa 'Yar Adua ya yi fama da ita.

Bayan rasuwar shugaba Yar'Adua an rantsar da Goodluck Ebele Jonathan a matsayin shugaban Najeriya kuma babban kwamandan askarawan kasar.

Dr. Goodluck Jonathan na da mata daya Dame Patience Jonathan da 'ya'ya biyu.