Wani bom ya fashe a arewa maso yammacin Iran

Wani bom ya fashe a arewa maso yammacin kasar Iran, inda mutane goma 'yan kallon faretin soja suka rasu.

Yawancin wadanda suka rasun yara kanana ne da mata.

Sun halarci faretinda ake yi ne a birnin Mahabad dake kusa da iyaka da yankin Kurdistan na Iraqi, domin bukin tunawa da zagayowar shekara ta talatin bayan kammala yakin Iran da Iraqi.

Kafar talabijin ta kasar Iran din ta watsa al'amarin kai tsaye.

Gwamnan yankin Vahid Jalalzadeh ya dora alhakin kai wannan hari, kan kungiyoyin dake adawa da juyin juya halinda aka yi a kasar.