Mulkin Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

A ranar 13 ga watan Junairun shekara ta 2010 ne wata babbar kotun tarayya ta umarci Goodluck Janathan da ya tafiyar da al'amuran shugabancin kasar yayin da marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua ke jiyya a kasar Saudiyya.

Ita ma majalisar dattawa ta amince da umarnin da kotun ta bayan a ranar 9 ga watan Fabreru na shekara ta 2010.

Duk da dawowar shugaba 'Yar Adua Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ya ci gaba da tafiyar da harkokin mulkin kasar a matsayin mukaddashin shugaban kasa, har zuwa ranar 6 ga watan Mayun shekara ta 2010 lokacin da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, bayan rasuwar Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua.

Jonathan ya kasance shugaban Najeriya na 14 tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Daga cikin ayyukan da ya ce gwamnatinsa zata fi maida hankali a kai sun hada da yaki da cin hanci da rashawa samar da wutar lantarki da kuma kawo gyara ga harkokin zabe a kasar.