Majalisa na duba hukunci kan sace jama'a

Majalisar wakilan Najeriya zata duba irin hukuncin da ya kamata a ce an zartar a kan wadanda aka samu da laifin sace mutane ko kuma garkuwa da su, domin neman kudaden fansa a nan gaba .

Kwamitin dake lura da harkokin shari'a na majalisar wakilan kasar shi ne ya bayyana haka yayin da ya kawo karshen kwanaki biyu da yayi , yana jin ra'ayoyin jama'a dangane da irin hukuncin da ya dace a yanke wa masu sace sacen jama'a a Najeriyar, lamarin da ya zamo ruwan dare a halin da ake ciki.

Shugaban Kwamitin, Hon Bala Ibn Na'Allah ya ce zasu gabatar da sakamakonsu ga majalisa, idan ta koma zama.