An bukaci Israila ta kara wa'adin daina gina matsugunnai

Image caption Mahalata taron tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta tsakiya

Bangarori hudun da ke jagorantar yunkurin zaman lafiya a gabas ta tsakiya sun yi kira ga Isra'ila da ta kara wa'adin da ta saka na daina gina matsugunnai a gabar yammacin kogin Jordan,wanda zai kare a karshen watan nan.

Shugaban Palasdinu Mahamoud Abbas dai ya sha nanata cewa zai kauracewa teburin sulhun idan Isra'ila ta cigaba da gina matsugunan.

Da ya ke jawabi a wata liyafar cin abincin dare a New York, shugaban kasar Isra'ila Shimon Peres ya ce wannnan karon ana iya cimma yarjejeniya ko don barazanar da yankin ke fuskanta daga Iran.

Ya ce babu wani a cikinmu da zai so ya ga Iran na mulkin gabas ta tsakiya. Larabawanmu da Yahudawanmu. Hanya daya da za'a kaucewa wannan barazana ita ce a tabbatar da sulhu.