Faransa ta dauki matakan ceto mutanenta da aka sace

An sace Faransawa guda ukku dake aiki a mahakar mai na cikin teku a Nigeria.

Wasu da ba a san ko su wane ne ba a cikin jiragen ruwan masu gudu suka sace mutanen a cikin jirginsu na kai kaya.

Babu wata kungiyar da tayi ikirarin kai hari kan jirgin mai suna The Bourbon, to amma mayaka a Nigeria dake kai hare hare a yankin Niger/Delta, sun saba yin amfani da irin wadannan dabaru na sace yan kasashen waje, domin neman gkudin fansa.

Bayan sace Faransawan a kasashen Niger da nigeria, kamfanin jirgin sama na kasar faransa wato Air France, ya bada sanarwar cewa yana daukar matakan kariya a kasashen Afirka biyar wadanda suka hada da Niger da Nigeria da Mauritania da Mali da kuma Chad, domin kare ma'aikatanta na kasa da kuma na cikin jirgi.

Tun farko Gwamnatin Faransa ta ce za ta dauki kowane irin mataki -- watakila da wadanda suka hada da matakin soji -- domin kokarin ceto maaikatan 7 da kungiyar Al-Qa'ida ta cafke daga wata mahakar ma'adinin Uranium a Niger.

Jiragen saman bincike na ta shawagi a sararin samaniyar hamadar Sahara domin kokarin gano su , kuma an tura dakaru zuwa yankin.

Ministan kula da harkokin waje na Faransa Bernard Kouchner ya ce, "ba abin mamaki ba ne, yadda muka gane cewa kungiyar Aqaeda ce kashin bayan sace mutanen. Yanzu da muka tabbatar da hakan, za mu ci gaba da tuntubar juna, wato Faransa da kawayenta na kasashen yankin Sahel da turai, kuma ina fata za mu yi iyakacin kokarinmu domin ganin an sako mutanen".