Amurka ta ce barazanar ta'addanci ta kara zama mai sarkakiya

Janet Napolitano, Sakatariyar harkokin cikin gidan Amurka
Image caption Janet Napolitano, Sakatariyar harkokin cikin gidan Amurka

Manyan jamian tsaro a Amurka sun ce barazanar da Amurka ke fuskanta daga kungiyar Alqaeda da magoyabayanta sun kara sarkewa. Manyan hafsoshin tsaro, sun shaidawa majalisar dattawan Amurka a Washington cewa adadin makarkashiyar hare hare ga kasar sun karu daga shekarar bara.

Sakatariyar hukumar tsaron Amurka na cikin gida Janet Napolitano ta bayyana cewa, "barazanar ta'addanci na habaka cikin gaggawa, kuma cikin shekarun da suka gabata, ta sauya salo da dama. Barazanar na sauya fasali a bangaren nau'o'in hare hare da dabaru".

Cibiyar yaki da ayyukan ta'addanci ta ce hare haren da ake shiryawa a cikin gida sun sake kai kololuwa , tun bayan sha daya ga watan satumban shekara ta dubu biyu da daya.

Sauyin da aka samu na matakan da ake dauka ana danganta su ne da yadda kungiyar Alka'idar ta yi asarar wasu yankunan da matattararta ne a Pakistan.