Jam'iyyar ANC ta ce bata tabuka komai ba

Jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta kudu ta yankewa kanta hukunci mai tsauri na cewa ba ta tabuka komai ba a kasar.

Wakilan jam'yyar dake halartar taron kolinta a birnin Durban sun amince da wani rahoto dake cewa tun bayan da shugaba Jacob Zuma ya karbi shugabancin jam'iyyar a shekara ta 2007 jam'iyyar ta samu koma baya ta bangaren rashin da'ar da baza 'a yadda da shi ba.

Wakilin BBC yace, Jam'iyyar ANC bata son ta ambato suna, to amma ana kyautata zaton anaiwa Julius Malema shugaban matasan jam'iyyar ne hannunka mai sanda.