Kungiyar kwadagon Faransa za ta yi zanga-zanga

Image caption Majalisar dokokin Faransa

Kungiyar kwadago a Faransa za ta sake gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da kudirin sauye-sauyen da za'a aiwatar kan tattalin arzikin kasar mai cike da rudani.

Yan kwadago sun ce za su dakatar da harkokin sufuri tare da rufe makarantu a fadin kasar.

Wannan dai shi ne karo na biyu a watan da muke ciki da ayyuka zasu tsaya cik, a kasar dangane da batun sauyen sauyen da za'a gudanar a tsarin fansho na kasar.

Ministan kwadagon kasar Eric Woerth ya ce gwamnatin kasar ba zata sauya matsayarta ba dagane da wannan batu.

Wakilin BBC ya ce ma'aikatan suna bukatar a kara musu haraji ne saboda idan aka zartar da kudirin , za'a dage shekarun aje aiki daga sittin zuwa sittin da biyu nan da shekarar 2018, tare kuma da dage shekarun fara karbar fansho zuwa sittin da bakwai.

Faransa dai kasa ce mai tarihin zanga zangar, jama'ar kasar basa barin abu ba tare da sun nuna rashin amincewarsu ba.