Gwamnatin India na taron gaggawa kan wasannin Commonwealth

Manmohan Singh, Praministan India
Image caption Manmohan Singh, Praministan India

Praministan kasar India, Manmohan Singh, ya kira wani taron gaggawa na majalisar ministocinsa, yayin da gwamnatin kasar ke ci gaba da fuskantar matsin lamba, na ganin ta kammala shirye shiryen karbar gasar wasannin Commonwealth a kan lokaci.

A yau ne tawagar farko ta 'yan wasa ke sauka a kasar ta India, duk kuwa da damuwar da ake nunawa, kan rashin kyaun masaukan da aka tanadar wa 'yan wasa.

Ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya a kasar, ya kara matsalar da masu shirya wasannin ke fuskanta a yanzu.