'Yan sanda sun kwato yaran da aka sace a Jos

A Nijeriya rundunar 'yan sandan jihar Filato ta ce ta yi nasarar kubutar da wasu yara 'yan gida daya da aka sace, shekaranjiya a Jos babban birnin jihar, aka kuma nemi mahaifinsu, Alhaji Awwalu Dan-Kurma ya biya kudaden fansa.

An sace yaran ne yayinda suke komawa gida daga makaranta, kuma yanzu haka an kama mutane uku da ake zargi da hannu a satar tasu, ciki har da direbansu.

An dai kubutar da yaran ne a wani gida dake unguwar 'yan Doya a birnin Jos.