Kasashe na nazari shekaru 50 bayan samun 'yancin kai

Tutar Najeriya
Image caption Tutar Najeriya

Wasu kasashe 16 da suka samu `yancin kai tare da Najeriya sun fara wani taro a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriyar, da nufin duba irin kalubalen da suka fuskanta a baya, da wadanda suke fuskanta yanzu, da kuma hanyoyin shawo kansu.

Gwamnatin Najeriyar ce ta shirya taron, a matsayin wani bangare na shagulgulan da take yi na cika shekaru 50 da samun mulkin kai daga Birtaniya, a ranar 1 ga watan Oktoban 1960.

Taron na samun halartar jami'an gwamnati da masana a fagen rayuwa daban-daban.