Obama ya yi gargadi kan muradun karni

Image caption Shugaba Barack Obama

Shugaba Obama ya yi gargadin cewa duniya ba za ta cimma muradun rage matsanancin talauci ba idan ba ta sauya yadda ta ke fuskanatar tallafi da kuma cigaban al'umma ba.

A jawabin da ya gabatar a majalisar dinkin duniya, ya baiyana cigaban al'umma a matsayin muhimmin abu ga dukkan kasashen duniya.

Ya ce mai da hankalin da suka yi kan bada tallafi ya ceci rayukan al'umma, a gajeren zango amma wanan ba cigaba ba ne, ya zamo dogaro kan wani.

Mista Obama ya ce cigaban da za'a samu a kasashe masu fama da talauci,zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arzikin da kuma tsaro a wasu kasashen duniyar wadanda suka hada da Amurkan.

Ya kuma ce ya zama dole a samarwa kasashen duniya hanyar da zasu kubuta daga talauci.