Obama yace akwai kalubale wajen sasanta Falasdinawa da Isra'ila

Obama a majalisar dinkin duniya
Image caption Obama a majalisar dinkin duniya

Shugaban Amurka Barack Obama ya amince cewar akwai babban kalubale a gabansa, a yunkurinsa na sasanta tsakanin Isra'ila da Palasdinawa.

Amma ya kara da cewa, akasin yin hakan na nufin ci gaba da zub-da-jini, wanda kuma ba za a lamunta ba.

Mr Obama ya bayyana haka ne lokacin wani jawabi da ya gabatar a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a New York.

Mr Obama yayi kira ga Falasdinawa da Isra'ila da su amsa wajibcin dake kansu na tarihi, sannan kuma duniya ta mara musu baya.

Da yake magana game da gine-ginen da take na 'yan kama wuri zauna, shugaba Obama yace wannan karon kamata ya yi a ci gaba da tattaunawar har sai an warware matsalar.