Makomar matasa a Najeriya

Cunkoson jama'a a Legas
Image caption Allah ya albarkaci Najeriya da dinbin jama'a musamman matasa

Najeriya kasa ce da Allah ya albarkace ta da dimbin jama'a musamman matasa, wadanda ake yiwa lakabi da manyan gobe.

Kuma irin wadannan matasa sune suka taka rawa wajen tabbatar da kafuwar kasar a baya.

Amma a daidai lokacin da kasar ke cika shekaru 50 da samun 'yancin kai sai dai wani rahoto da Cibiyar bunkasa al'adun Burtaniya ta wallafa ya nuna cewa matasan kasar na fuskantar mummunar makoma muddin dai kasar bata dauki wasu matakai na azo agani ba.

Najeriya za ta iya fuskantar habakar tattalin arziki idan aka samar da makoma mai inganci ga dinbin matasan kasar, sai dai akwai babbar matsala idan aka gaza.

Ana sa ran gudummawar da matasa za su iya bayarwa wajen ci gaban kasar ita ya kamata mahukunta su maida hankali a kai maimakon dogaro da man fetur.

Hakan ka iya zamowa mihimmin mataki ga kasar a karni na 21.

Rahoton ya nuna cewa makomar kasar ta dogara ne kan irin halin da matasan za su samu kansu a ciki nan da 'yan shekaru masu zuwa.

Najeriya ta dade tana fama da matsalar banbance tun bayan samun 'yancin kai.

Habakar jama'a cikkin sauri ta zamo wani babban kalubale ga ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma tsare-tsaren siyasa dana zamantakewa.

A shekaru 30 da suka wuce tattalin arzikin kasar ya fuskanci koma baya, musamman idan aka kwatanta da kasashen da suka taso tare irinsu Indonesia.

Shekarun 1990 su ne mafiya muni a tarihin kasar, inda bunkasar tatalin arzikin kasar ya gaza na shekarun 1980.

Rawar da matasa suka taka a baya

A baya dai matasa sun taka rawa sosai a sassa daban-daban na ci gaban Najeriya.

Kusan za a iya cewa su ne kan gaba wajen tafiyar da al'amuran kasar bayan samun 'yancin kanta.

Alal misali, shugabanni irinsu Janar Murtala Muhammad da Janar Yakubu Gowon, sun shugabanci kasar suna matasa, duk da cewa dai shuagabanci ne na soji, amma wasu na ganin sun taka rawar gani.

Haka kuma ko a yanzu akwai mutane irinsu kakakin Majalisar Wakilai ta kasa Dimeji Bankole, wanda shi ma matashi ne.

Sai dai wasu na ganin a yanzu matasan ba su da makoma mai kyau, ganin cewa 'ya'yan wane-da-wane ne kawai ke iya samun damar yin ilimi mai inganci, saboda kusan baki dayan makarantun gwamnati ba sa tafiya yadda ya kamata.

Fata-na-gari

Najeriya na da damar motsawa gaba idan mahukunta suka yi amfani da damar dake akwai na farfado da tattalin arzikinta da inganta harkokin lafiya.

Hakan zai iya sanya adadin kudaden da jama'a ke samu ya ninka da kashi uku nan da shekara ta 2030.

Amma idan har kasar ta kasa cimma wadannan manofofi a cewar rahoton, to za ta fada cikin mummunar matsala, wadda ka iya sanya makomar miliyoyin matasanta cikin rudani. A wani abu da ake ganin zai iya yin muni sosai, kasar za ta iya fuskantar karuwar matasan da ba su da ayyukan yi; karuwar neman aikin yi da iko kan filaye da kuma albarkatun kasa da gwagwarmayar siyasa; biranen da ba za su iya daukar nauyin da wadannan matsaloli za su haifar musu, ka iya samun kansu cikin rikicin addini da na kabilanci.

Image caption Matasa sun taka rawar gani wajen samun 'yancin kan Najeriya

Masana dai na ganin idan har kasar bata dauki matakan shawo kan matsalar banbance banbance tsakanin 'yan kasar ba, to akwai yiwuwar ci gaba da samun tashe-tashen hankula.

Matasan Najeriya dai na fama da karancin ababen more rayuwa, wadanda takwarorinsu na sauran kasashen duniya ke samu musamman a wannan karni.

Karancin ayyukan yi na barazana ga makomar matasa a kasar, wadanda ke samar da abubuwan da suke amfani da su na shekara 30 kawai, idan aka kwatanta da takwarorinsu na Indonesia 34, India 35, sai kuma matasan China dake samarda 37.

Ganin cewa kasar ta cika shekaru 50 da samun 'yancin kai, abin da ya fi jan hankalin jama'a a yanzu shi ne, shin ko mahukunta a kasar za su iya amfani da wannan damar da suke da ita wajen amfani da dinbin matasan da Allah ya albarkaci kasar da su, wajen ciyarda kasar gaba.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kasashen ke kokawa da rashin matasan da za su taimaka wajen ciyar da tattalin arzikinsu gaba.