Prince Johnson zai tsaya takara a Liberia

Tutar Liberia
Image caption Tutar Liberia

Tsohon madugun 'yantawaye a Liberia, Prince Johnson, ya kare aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan Nuwamba.

Prince Johnson ya bayyana cewa a wadansu kasashe shugabannin soja sun zama shugabannin kasa don haka ba wani aibi idan hakan ta faru a Liberia.

Prince Johnson ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar ne bayan Hukumar Zabe ta Kasa a Liberia ta bayyana cewa jam'iyyarsa ta National Union for Democratic Progress ta cika dukkan sharuddan da ake bukata don shiga zaben.

A shekarar 2005 ne dai aka zabi Prince Johnson da gagarumin rinjaye zuwa Majalisar Dattawa ta Liberia.

Tsohon madugun 'yan tawayen ya yi kaurin suna ne a lokacin yakin basasar kasar ta Liberia, musamman saboda irin ukubar da ya ganawa shugaban kasar na wancan lokacin, Samuel Doe, kafin kashe shi daga bisani a shekarar 1990.

Wani hoton bidiyo ya nuna Mista Johnson yana shan barasa lokacin da ya umurci mabiyansa su yanke kunnuwan Samuel Doe.

Masu fafutkar kare hakkin bil-Adama dai na adawa da takarar ta Prince Johnson, wadda suka ce za ta iya sake jefa kasar cikin yakin basasa.

Tsohon madugun 'yan tawayen dai zai yi takara ne da Shugaba Ellen Johnson Sir-Leaf da kuma mashahurin dan wasan kwallon kafar nan George Weah.