Najeriya za ta yi amfani da kafafen watsa labarai don samun karbabben zabe

Majalisar lura da watsa labarai da sadarwa ta Najeriya ta soma taron ta, karo na 41 a Sakkwato, domin yin nazari kan irin rawar da kafofin yada labarai ke takawa a zabubuka a kasar.

Da yake bude taron, ministan kasa a ma'aikatar watsa labarai da sadarwa, Mr Labaran Maku, yace taron zai mayar da hankali ne kan yadda kasar za ta yi anfani da watsa labarai da kuma sadarwa yadda ya kamata, wajen gudanar da karbabben zabe a shekara mai zuwa.

Kafafen yada labarai na taka mahimmiyar rawa kan yadda ake gudanar da zabe a Najeriyar.