Amurka ta fice yayin jawabin Ahmadinejad

Shugaba Ahmadinejad na Iran
Image caption Shugaba Mahmud Ahmadinejad na Iran

Wakilan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya sun fice daga babban taron majalisar lokacin da Shugaban Iran, Mahmud Ahmadinejad, ke jawabinsa.

Jawabin na Shugaba Ahmadinejad dai ya kunshi ra'ayoyinsa ne a kan batutuwan da suka hada da cewa tsarin jari hujja na durkushewa don haka ana bukatar wani sabon tsarin shugabanci a duniya.

A cewarsa, ya kamata salihan mutane masu halaye irin na annabawa su shugabanci duniya.

Shugaban na Iran ya kuma ba da misalign abubuwan da suka addabi duniya, inda ya bayar da misali da abubuwan da suka biyo bayan hare-haren ranar 11 ga watan Satumban 2001, yana mai cewa an yiwa abin da ya wakana fassarori iri-iri, ciki har da cewa mai yiwuwa Amurka ce da kanta ta kitsa al'amarin don ta bayar da kariya ga Isra'ila.

A daidai wannan lokacin ne wakilan Amurkan suka tashi suka kuma fice daga dakin taron, wakilan kasashe talatin da uku na rufa musu baya.

Wakilan da suka fice sun hada da na dukkan kasashen Tarayyar Turai, da na Canada, da na Australiya, da na New Zealand, da kuma na Costa Rica.

To amma hakan bai sa Mista Ahmadinejad ya yi ko gezau ba; inda ya ci gaba da kakkausar suka a kan Isra'ila.

Dangane da batun nukiliya kuwa, Mista Ahmadinejad cewa ya yi makamashin wata baiwa ce daga Ubangiji, kuma wadanda ke sanyawa Iran takunkumi na tuntsurar da dan sauran mutuncin da Majalisar Dinkin Duniya ke da shi.