China na neman diyya a hannun Japan

Matukin jirgin ruwan kamun kifin da Japan ta kama
Image caption Matukin jirgin ruwan kamun kifin da Japan ta kama

China ta bukaci Japan ta nemi gafararta ta kuma biya diyya saboda tsare matukin wani jirgin ruwan kamun kifi dan China da ta yi.

Mutumin dai ya isa gida bayan masu shigar da kara na Japan sun sako shi.

Matukin jirgin ruwan kamun kifin ya bar Japan ne cikin dare a wani jirgin sama da gwamnatin kasar China ta yi shata musamman don ya dauke shi.

Sakin mutumin dai ya zo ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin kasashen—wadanda suka fi karfin tattalin arziki a nahiyar Asiya—ta yi tsami fiye da ko wanne lokaci a shekaru da dama.

Sanadiyyar tsare mutumin dai, China ta yanke hulda da Japan a wani mataki, yayinda 'yan yawon shakatawa da dama daga China suka fasa kai ziyara Japan din.

Lokacin da suke yanke shawarar sakin mutumin, masu shigar da kara na Japan sun yi la'akari da wannan batu.

Masu shigar da karar sun ce ko da yake mai yiwuwa da gangan matukin jirgin ruwan kamun kifin ya yi karo da jiragen jami'an tsaron ruwan Japan, suna ganin tsare shi bai dace ba idan aka yi la'akari da dangantakar da ke tsakanin kasashen.

Gwamnatin Japan dai ta nace cewa bisa radin kansu ne masu shigar da karar suka saki mutumin; to amma 'yan adawa sun yi suka a kan matakin, suna masu cewa hakan ya nuna raunin kasar ta Japan.

China ta ce tsare mutumin ya keta mutuncinta a matsayinta na kasa.

Ta kuma jaddada cewa tsaunukan da al'amarin ya auku daura da su, wadanda ke karkashin ikon Japan, mallakinta ne.

Karin bayani