Ambaliya ta raba mutane miliyan 2 da gidajensu

Ambaliyar ruwa a Jihar Jigawa
Image caption Kwanakin baya ma Jihar Jigawa ta yi fama da ambaliyar ruwa

Jami'an gwamnati a arewacin Najeriya sun ce mutane miliyan biyu ne ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu bayan an bude wadansu madatsun ruwa biyu da suka cika suka batse kuma ake fargabar za su ci yankunan da ke kusa da su.

Ruwan da ya fito daga madatsun ruwan Callawa da Tiga a Jihar Kano dai ya malala zuwa yankunan da ke kwari a Jihar Jigawa.

Yanzu haka dai ana ci gaba da tsugunar da mazauna kauyukan da ambaliyar ruwan ta shafa.

Jihohi da dama na Najeriya ne dai suka fuskanci ambaliyar ruwa sakamakon dimbin ruwan saman da aka samu cikin watanni biyu.