Ambaliyar ruwan Jahar Jigawa

Ambaliyar ruwa Jahar Jigawa
Image caption Mahukuntan jahar Jigawa na shirye shiryen kwashe al'ummomin dake zaune a wasu yankunan da ake samun yawaitar ambaliyar ruwa

Hukumomi a jihar Jigawa dake arewacin Najeriya sunce suna shirye shiryen kwashe al'ummomin dake zaune a wasu yankunan da ake samun yawaitar ambaliyar ruwa, bayan da ambaliyar ruwan tayi sanadiyyar rasa matsugunai ga kimanin mutane miliyan biyu.

A wata hira da BBC Kwamishina a ma'aikatar yada labarai ta jihar Aminu Mohamed Gumel ya ce an bude wasu madatsun ruwa biyu da suka cika suka batse wadanda kuma suka mamaye kauyukan dake kusa, bayan fargabar da ake yi cewa madatsun ruwan ka iya fashewa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da akayi ta shararawa na kusan watanni biyu.

Ya kuma kara da cewa tuni hukumomi suka taimakawa al'ummomin da wannan al'amari ya shafa ta hanyar samar masu da matsugunai na wucin gadi tare da abinci da kuma tsabtataccen ruwan sha.