Ed Miliband ya zama sabon shugaban jam'iyyar Labour

Sabon shugaban jam'iyyar labour Ed Miliband
Image caption Jam'iyyar labour a Burtaniya ta zabi sabon shugabanta Ed Miliband wanda ya kada dan uwansa David Miliband

Jam'iyyar adawa ta Labour a Burtaniya ta zabi tsohon ministan mai kula da yanayi Ed Miliband, a matsayin sabon shugabanta.

Mr Miliband, mai shekaru arba'in wanda ya kayar da yayansa, tsohon sakataren harkokin wajen Burtaniya David Miliband, ya ce yanzu zamani ne na sabbin jini.

Mr Miliband ya bayyana cewar sakonsa ga burtaniya shine, yace ya san martabar kasar ta ragu, don haka yace yasan ana bukatar samun canji.

Ya kara da cewar 'yau sabbin jini sun karba ragamar shugabancin jam'iyyar Labour wadanda suka fahimci bukatar a samu sauyi'.

Daya daga cikin muhimman kalubalen dake gaban jam'iyyar ita ce ta dauki matakai dangane da shawarar rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa da gwamnatin hadin gwiwa na Conservative da Liberal Democrat ta yi.