Taron sasanta Isra'ila da Falastinawa

Shugaba Mahmoud Abbas tare da Shugaba Barack Obama
Image caption Shugaban Falastinawa Mahmoud Abbas ya bayyanawa zauren majalisar dinkin duniya cewar tilas Israila ta zabi tsakanin matsugunai da kuma zaman lafiya

Shugaban Falastinawa Mahmoud Abbas ya ce tilas Isra'ila ta zaba tsakanin matsugunai ko kuma zaman lafiya.

Shugaba Mahmoud Abbas ya bayyana haka ne a zauren babban taron Majalisar Dinkin Duniya kwana guda kafin cikar wa'adin dokar hana fadada matsugunai a gabar tekun Jordon.

Koda yake shugaba Abbas bai nuna wata alama ba a jawabinsa da ya nuna cewa ko Falasdinawa sun sauya aniyarsu ta ficewa daga tattaunawar sulhu da aka farfado da ita, matukar Israila bata kara wa'adin ba.

Kasar Amurka dai na jagorantar yunkurin gaggawa na karshe don sasanta bangarorin biyu.