Da sauran aiki wajen gyara masaukin 'yan wasa a Delhi

Masaukin 'yan wasan Commonwealth a Delhi
Image caption Masaukin 'yan wasan Commonwealth a Delhi

Wata babbar Minista a Indiya, Sheila Dixit, ta ce kauyen da ake ginawa na musamman domin wasannin motsa jiki na Commomwealth, ba za a kammala shi ba har sai ranar laraba.

Wannan sanarwar ta biyo bayan irin sukar da Indiyar ke sha, kan yadda take gudanar da shirye-shiryen gasar ta kasashen Commonwealth, wadda za a fara a ranar Lahadi mai zuwa.

Mutane dubu 4 ne ke aiki dare da rana a wurin da za a saukar da 'yan wasa, domin yin dimbin gyare gyare.

Wasu daga cikin 'yan wasa sun ce ba za su shiga gasar ba, saboda abinda suka kira tsananin kazanta a masaukin da aka tanadar masu.